Wednesday, 20 November 2013

WALIYYIN ALLAH

Waliyyi shi ne wanda ya yi imani da Allah, yake
kuma jin tsoronsa, kamar yadda Allah
Madaukakin Sarki ya fada a cikin littafinsa mai
girma, Suratu Yunus aya ta 62 - 63.
Dukkan musulmi mai tsoron Allah waliyyin Allah ne, gwargwadon imaninsa gwargwadon
walittakarsa, mafiya darajar waliyyai Annabawa
da Manzannin Allah, sai Sahabban Annabi
(S.A.W), Siddikai, shahidai sai Salihan bayi.
Babu wani zamani ko lokaci tun farkon zuwan
musulunci har zuwa daf da tashin Alkiyama da babu waliyyan Allah a cikinsa. Akwai waliyyan
Allah Mata kamar yadda ake samunsu a maza,
akwai waliyyan Allah a cikin malamai da masu
Mulki, da yan kasuwa, da talakawa da masu
kudi.
Ahlussunnati Wal Jama'a sun yi imani da samuwar waliyyan Allah, har ma karamominsu,
kamar yadda Alkur'ani da Hadisai ingantattau
suka tabbatar da hakan.
Walittaka bata haduwa da yin shirka da bokanci
ko da'awar komai Allah ne, duk wanda dayan
wadannan abubuwa na shirka ko bokanci ko da'awar komai Allah ne ya tabbata a kansa to
wannan ba waliyyin Allah ba ne, sai dai waliyyin
Shaidan.
Kuskure ne babba takaita waliyyan Allah akan
wasu mutane ko jama'a ko darika, a ce kadai a
cikinsu ake samun waliyyai. Haka nan kuskure ne ayyana wasu mutane ko mutum a ce duk
wanda baya sonsa ko baya son su, baya son
waliyyai, ko yana gaba da waliyyai, ko bai yarda
da waliyyai ba. Haka nan kuskure ne babba fitar
da sahaban Manzon Allah daga waliyyan Allah,
har a rika ganin mai kaunarsu baya son waliyyai, mai zaginsu da aibata su masoyin waliyyai ne,
tunda dai ya yarda da wasu mutane da ake
kirawa walittaka.
Kofar walittaka a bude take, babu wani mutum
da zai zama cikamakin waliyyan Allah, duk
wanda ya yi da'awar shi ne cikamakin waliyyai a yau ko a zamanin baya, hakika ya yi kuskure,
kuma ya fadi abin da ba haka yake ba,
cikamakin waliyyai shi ne karshen mumini da zai
bar wannan duniya. Allah ya sanya mu cikin
waliyyansa na gaskiya, masu kaunar waliyyan
gaskiya, Annabwa da Siddikai da Salihan bayi. Ameen.

No comments:

Post a Comment