Tuesday, 26 November 2013

BIYAYYAN MAI BIYAYYA, KO SA'BON MAI SA'BO, BAYA RAGYE KOMAI A CIKIN MULKIN ALLAH

Daga Abi Zarrin Al-Gifariyyu (RA) Daga Manzon
Allah (SAW) cikin irin abin da ya ke ruwaitowa
daga Allah cewa: Allah Yaa ce, "Yaa ku bayina!
hakika na haramta wa kaina zalunci ku ma na
haramta shi gare ku, to kada ku yi zalunci. Yaa
ku bayina! dukkanku 'batattu ne, sai wanda na shiryar. To, ku nemi shiriyata in shiryar da ku.
Yaa ku bayina! dukkanku mayunwata ne, sai
wanda na ciyar, to ku nemi ciyarwata in ciyar da
ku. Yaa ku bayina! dukanku huntaye ne, sai
wanda na tufatar. To, ku nemi tufarwata in
tufatar da ku. Yaa ku bayina! hakika kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai
baki daya. To, ku nemi gafarata, in gafarta muku.
Yaa ku bayina! ba za ku iya cutar da ni ba, balle
ku cuce ni, kuma ba ku isa amfanata ba, balle ku
amfane ni. Yaa ku bayina! da dai tun daga na
farkonku har ya zuwa na karshenku, da mutanenku, da Aljannunku, za su yi dai-dai da
zuciyar mafi tsoron Allanku, wannan ba zai 'kara
kome a cikin mulkina ba. Yaa ku bayina! da dai
tun daga na farkonku har ya zuwa na karshenku,
da mutanenku, da Aljannunku, za su yi dai-dai
da zuciyar mafi ashararancinku, wannan ba zai rage kome daga mulkina ba. Yaa ku bayina! da
dai tun daga na farkonku har ya zuwa na
karshenku, da mutanenku da aljannunku, za ku
taru a wuri guda, sannan ko wane 'daya ya roke
ni, ni kuma inba wa ko wane daya bukatarsa,
wannan ba zai ragye kome daga abin da na mallaka ba, sai kamar yadda allura za ta ragye
in an tsoma ta cikin kogi. Yaa ku bayina!
ayyukanku ne kurum nake 'kidaya muku, sannan
inba ku ladansu. To! wanda duk ya sami alkhairi
sai ya gode wa Allah, wanda kuwa ya sami
wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa". [Musulim].

No comments:

Post a Comment