Tuesday, 26 November 2013

KIWON LAFIYA TA FUSKAR SANA'O'INMU

A haqiqanin gaskiya ba sana’ar da ba ta qunshe da gajiya da haxurra ga lafiyarmu sai dai wata ta fi
wata. A aikin walda ba idanu ne kaxai suke shan wahala
ba ga mai walda, duk inda tartsatsin narkakken qarfe ko
dalma ta tava a jikinka akwai illa ko dai ta quna ko wani
abu daban. Dole ke nan mai walda ya tanadi kayan da
za su rufe jiki gaba-xaya, domin kiyaye waxannan, muhimmi daga ciki shi ne gilashin rufe fuska gaba xaya
ba tabarau na ido kaxai ba. Kuma ba qanshin gaskiya a
ce wai ba zai tsufa da idonsa qalau ba, ko gajiyar sana’a
na tashi.
Sauran misalan da zan ba ku a xaya vangaren
tambayar, na irin wahalhalun da ke tattare da sana’o’inmu sun haxa da:
Noma: Wanda ake ce wa naduqe tsohon ciniki. Wataqila
saboda wahalarsa ce a yanzu yake nema ya zama tarihi.
Matsalolinsa sun haxa da yawan ciwon baya, kantar
hannu, shiga haxarin cizon qwari da dabbobi irinsu
kunama da maciji da sauransu. Sauran su ne saurin samun ciwon qaba, ko kwasar qwayoyin cuta a
kududdufai idan an je wanke jiki, qwayoyi irin masu
kawo tsargiya, kurkunu, dundumi da sauransu. Noman
zamani da ake yi ta hanyar na’urori kamar motar huxa
da ta shuka da ta girbi duk ba su tattare da irin wannan
haxari. Kiwo: Shi ma xan uwan noma ne kuma duk haxarin
noma zai iya shiga haxarin kiwo. Bugu da qari kuma ga
haxarin kamuwa da cututtukan dabbobi irinsu ciwon
barci ko sammore, wanda qudan tsando ke kawowa, ko
tarin TB na dabbobi da sauransu.
Su: Masunta suna cikin haxarin lumewa cikin ruwa ko shan gurvataccen ruwa mai qwayoyin cuta da kamuwa
da qwayoyin cuta irinsu tsargiya.
Jima: A yanzu da yake kamfanonin jima sun yi qaranci,
an xan rage samun cututtukan da ke faruwa sanadin
wannan matsala. Yawanci qwayoyin cuta ne ke taruwa
a kan fata idan an zo wanke su a kwashe su. A inda kamfanunnukan fata suka rage a kodayaushe
magudanan wurin ba sa rabo da ruwa mai wari wanda
ke xauke da nau’ukan qwayoyin cuta iri-iri, waxanda
kan iya shiga ruwan gari ta fasassun bututu, a samu
cututtukan ruwa irinsu amai da gudawa.
Rini: Marina suna xaya daga cikin mutanen da suka fi samun ciwon daji na mafitsara da dangoginsu,
sakamakon sinadaran haxi na yin rini. Wato shi tirin da
ake jiqawa wasu masana sun tabbatar yana iya kawo
ciwon daji.
Qira: Maqera kuma sun fi shiga haxarin raunuka da
qarafuna da quna daga garwashin wuta. Tuqi: A yanzu wannan sana’a ita ce za a ce ta fi kowace
sana’a haxarin cutarwa da ma rasa rayuka, domin nasu
kullum ne. Direbobi ko da ba ma na sana’a ba,
musamman masu tuqin nesa sun fi kowa samun karaya
da buguwa da sauran matsaloli na haxarurrukan qarfe
irinsu mutuwar wani vari na jiki da sauransu. Sana’ar wasanni: Duk da cewa wasanni na motsa jiki
suna xaya daga cikin sana’o’i masu gyara jiki da qara
lafiya, da wuya a samu cikakken xan wasan da bai tava
samun karaya ko targaxe ba.
Gini Da Injiniyanci: Magina da injiniyoyi suna xaya daga
cikin mutane masu samun haxurra su ma na buguwa da cutuwa daga injina ko matsalar kunne idan inji yana da
qara. Shanyewar sashen jiki sakamakon faxowa daga
sama ko kuma wani abu ya faxo wa mutum daga sama
kan faru. Ruwan fenti, wannan yana da sindarin dalma
da zai iya kawo illa ga lafiya.
Sayar da Abinci: Masu sayar da abubuwan ci da na sha kamar masu masu qosai da ma masu dafa abincin
sayarwa a gida waxanda suke amfani da murhu, suna
xaya daga cikin waxanda hayaqin itace ke wa illa a
huhu. An qiyasta cewa bayan taba sigari, masu girki a
gaban murhu su ne kan gaba wajen matsalolin huhu. Ba
nan hayaqin ya tsaya ba, yakan yi illa a ido ma. Kanikanci: Yawanci bakanikai ba wai datti ba ne yake sa
jikinsu da kayansu baqi, baqin mai ne kawai. Suna cikin
haxarin samun dusashewar fata dalilin wannan mai,
saboda ba kowane sabulu ba ne ke iya wanke shi amma
ban da duhun, ba wata illa yake ga ita fatar ba. Sai dai
duk da haka yana da kyau su ma su riqa rufe duka fatar tasu da dogayen kaya da sanya safar roba a
hannayensu, domin da dama haka suke cin abinci da
hannun ba tare da sun wanke su sosai ba, tunda duk
inda aka samu maiqo za a samu qwayoyin cuta.
Wanki da guga: Masu sana’ar wankau su kuma sun fi
kowa samun matsalar cin ruwa a fata saboda yawan hulxa da ruwa, sai kuma cin fata da sabulai ko omo kan
yi.
Ma’aikatan Ofis da ’Yan kasuwa: Masu iya magana suka
ce wai ‘zama wuri xaya tsautsayi inji kifi.’ Wannan
tsautsayi ba kan kifi kawai ya tsaya ba, waxanda suke
da sana’ar zama wuri guda na tsawon lokaci kamar masu aikin ofis da yawa-yawan ’yan kasuwa su kuma
sun fi kowa shiga haxarin kamuwa da cututtukan qiba
da na hawan jini da cututtukan zuciya saboda rashin
kazar-kazar, saboda ban da yawan zaman kuma kusan
sun fi kowa son cin ‘daxi.’
Aikin lafiya: A qarshe mu ma ba a bar mu a baya ba wajen samun matsalolin lafiya a wuraren aiki. Mu ma
namu haxurran ba qanana ba ne. Duk wanda ya zo da
qwayoyin cuta, yawanci a kanmu yake baje su, kamar
na tarin fuka da mura, ban da haxarin kamuwa da
cututtukan cikin jini irinsu qanjamau da ciwon hanta da
yawanci masu fixa ko xibar jini kan samu. Masu gajen haquri a dangin marasa lafiya a kanmu suke huce
haushinsu wajen faxa da masu jiyya har ma da bugun
kawo wuqa, duk da cewa wasunmu mu ma muna da
hannu wajen jawo faxa.
Waxannan misalai ne kawai, domin ba a tavo wasu da
dama ba irin masu sana’ar aikin ba-haya ba da masu sayar da fetur. Kowa idan ya tuna sana’a zai iya fito da
haxarin da ke tattare da ita. A taqaice dai duk inda ka
duba za ka ga akwai haxari ga lafiya tattare da kowace
sana’a, sai dai kawai a riqa xaukar matakan kariya daga
duk abubuwan da aka zayyana ga kowace sana’a,
wanda mun san masu karatun wannan shafi yanzu qwararru ne a wannan vangare. Mai aikin qarfi zai iya
shan maganin ciwon jiki irinsu panadol amma ban da
masu sa nacin sha da maye irinsu tramol.
(by doctor auwal bala)

No comments:

Post a Comment