Tuesday, 26 November 2013

MENENE YA ZAMA WAJIBI A KAN MU DANGANE DA SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W)?

Abin da ya zama dole a kan mu ga sahabban manzo Allah
(s.a.w) shine son su da neman Allah ya yarda da su, da
kuma kubutar da zuciyarmu da bakunanmu daga cutar da
su, da kuma yada falalarsu, tare da kamewa daga
mummunan abin da ya faru a tsakaninsu; Domin su ba
ma'asumai (mara sa laifi) ba ne, sai dai su masu kokari ne (Mujtahidai masu binciken gaskiya da nemanta). Duk
wanda ya dace daga cikinsu yana da lada biyu, amma idan
ya yi kuskure ya na da lada daya a kan kokarinsa
(Ijtahadinsa). Kuskurensa kuma an gafarta masa. Kuma
suna da kyawawan ayyuka wandanda za su tafiyar musu
da munanan da suka auku daga gare su, in ya auku. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "kar ku zagi sahabbaina, na
rantse da wanda raina ke hannunsa, da a ce dayanku zai
ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinare, ba zai kai
ciyarwar dayansu na mudun ko rabinsa ba." (Bukhari da
Muslim)
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wadda ya zagi sahabbaina to la'anar Allah da Mala'iku da mutane gaba
daya sun tabbata akansa" (twabarani)

No comments:

Post a Comment