Saturday, 30 November 2013

HAKKIN MUSULMI AKAN 'DAN UWANSA, GUDA SHIDA NE:

1. Idan ka hadu dashi kayi masa sallama. 2. Idan ya gayyaceka zuwa wani sha'aninsa, to ka amsa
masa gayyatar. 3. Idan ya nemi nasiha daga gareka, to kayi masa. 4. Idan yayi atishawa, kuma yayi Hamdala, to kayi masa
addu'a. 5. Idan bashi da lafiya kaje ka dubashi (ka gaishe shi). 6. Idan ya rasu, kayi masa rakiya. (Kabi jana'izarsa zuwa
makabarta).

FA'IDODIN HABBA2SSAUDA'I

21. Mace MAI CIKI ta rika zuba cokali 5 na garin H/sauda
acikin zuma kofi guda. tana shan cokali 2 sau uku kullum.
Insha Allahu zata haihu lafiya. kuma Allah zai kiyaye mata
jaririnta daga Quraje ko cutar daji. 22. Wanda yake fama da matsalar yawan fitar da Maziyyi
ba abisa Ka'ida ba, idan yana shan H/sauda cokali 1 kullum
da safe acikin shayi tare da lemon tsami za'a dace. 23. Wanda yake fama da matsalar KAUSHIN HANNU KO
QAFA, ya mulke hannun ko kafar da man H/sauda da
daddare kafin ya kwanta. Idan ya farka kuma, bayan yayi
sallar asuba, sai ya samu dutsen goge kaushi ya durje
kafar ko hannun..
Sanna idan yayi wanka zai fita, sai ya sake mulkewa Kafar ko hannun. Ya maimaita haka kwana 5 ko 7. NSHA ALLAHU
kafarsa zata koma sumul sumul. 24. H/sauda tana maganin Ciwon ido. idan aka nikata
Lukwi sai a hada da tozali arika shafawa. Insha Allahu za'a
samu lafiya. 25. Idan yaro yana yawan firgita, ko kukan dare, ko Rashin
barci, asamu man H/sauda atofa ayatul kursiyyi Qafa 7 da
falaki da naas arika shafa masa ajikinsa.INSHA ALLAHU zai
dena. 26. Hakanan Masu ULCER su samu Man h/sauda chokali
7atofa AYATUSH SHIFA'I tare da Fatiha 7, Qulhuwallahu 41.
Sannan agaurayashi acikin Zuma kofi 1. sai arika shan
cokali 3 kafin breakfast da kuma kafin abincin dare.
amma za'a sha ne minti 15 kafin cin abinci. ALLAH SA MU DACE.

Thursday, 28 November 2013

KYAKYKYAWAR NIYYA BAYASA AIKI YA KARBU SAI IN AIKIN YA DACE DA KOYARWAR MANZON ALLAH (S.A.W)

domin Allah baya karban aiki sai da niyya,amma niyya
kadai bata sa aiki ya zama kyakykyawa sai kuma in aikin
ya zama Manzon Allah ne ya koyar dashi,wannan
kyakykyawar niyyar ba zata tseratar da aikin ba.
Mutum ne zayyi sallar Azahar sai yayi raka'a shida,ka
tambaye shi yace kyakykyawar niyya yayi, alheri nakeso in kara,shiyasa na kara raka'a biyu,shin kyakykyawar
niyyarsa zata tseratar da sallar ta zama karbabbiya? Babu
yadda za'ayi a amsa,saboda ba haka Manzon Allah ya
koyar ba.Yazo azumin ramadan sai yayi 32 aka tambaye
shi meyasa kake azumi yau sallah,sai yace ai so nakeyi
nawa yafi na kowa,shin kyakykyawar niyyarsa sai yasa aikin ya zama karbabbe? Babu yadda za'ayi haka ya yiwu.
Ashe kenan kyakykyawar niyya ba yasa aiki ya karbu sai in
aikin ya dace da koyarwar Manzon Allah (S.A.W).Don haka
zaka samu dayawa daga cikin masu yin bidi'a suna da
kyakykyawar niyya amma inda yayi kuskure shine hanyar
yin aikin.Ita kuwa niyya daban hanyar aiwatar da aiki daban.
Idan hanyar aiwatar aiki tayi kyau, to sai kayi kyakykyawar
niyya abu biyu in sun hadu sai aiki ya zama
karbabbe,amma kana da kyakykyawar niyya amma
hanyar aiwatar da aikin bayi da kyau Manzon Allah bai
koyar ba aikin bazai zama kyakykyawa ba,domin niyyar ka bata da kyau,kayi niyya ne don wanin Allah,Allah bazai
karba ba,koda kuwa aikin irin na Manzon Allah ne (S.A.W).
Sai Abu guda biyu sun hadu da juna don akan wannan ne
aka ma Gina addinin.An ginata ne akan kalmar "LAILAHA
ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH (S.A.W)".Kalmar
'LAILAHA ILLALLAH' Tana nufin kada ka bautawa kowa sai Allah,kuma don shi zakayi Ibadar.kalmar 'MUHAMMADUR
RASULULLAH' Tana nufin kada kayi Ibada sai yadda ya
koyar.Ko Allah ka bautawa da abinda Manzon Allah baizo
dashi ba,Allah bazai karba ba,kuma ko abinda Manzon
yazo dashi ne amma sai ka bautawa Allah da niyyar ka
gwama shi da wani shima Allah bazai karba ba.Ashe wainnan abubuwa biyu dole mu yarda dasu,mu kuma
karbe su. 'YAN'UWANA WALLAHI BAMA NUFIN MUSGUNAWA
WANI IYAKA MUDAI MU FADI GASKIYA MU KUMA GYARA
MUKU,BAMA NUFIN TOZARTA WANI,DON HAKA MU GYARA
AYYUKAN MU DON ALLAH KO MA SAMU BABBAN RABO

Tuesday, 26 November 2013

FA'IDODIN HABBATUS SAUDA πππππ√πππππππππππππππππππ

Binciken Manyan Likitocin zamani ya tabbatar da
cewar: Habbatus Sauda tana Qarfafa Garkuwar Jiki. don
haka ana kyakyawan zaton cewar masu fama da chutar
AIDS idan suna amfani da ita (mai ko gari) zasu samu
Qarin lafiya sosai ajikinsu.

Asamu zuma mai yawa (kamar kofi 3) asanya garin H/
sauda cokali 7 garin Zaitun cokali 4. Garin zogale cokali 3.
Asanya citta da kayan Kamshi aciki. sannan agauraya arika
shan cokali 2 safe da rana da yamma kafin cin abinci.
(Wannan fa'ida zatayi amfani ga masu fama da cutar AIDS,
cutar SIKILA, TYPOID FEVER, etc.)
abbatus Sauda tana maganin kurarrajin Baki dana
Makogoroil isan ana kurkura bakin da ita kuma ana
hadiyanta bayan an dumamata kadan. 13. HABBATUS SAUDA tana maganin matsalar TSAKUWAR
MARA, APPENDITIXS, da sauransu. idan ana shanta da
zuma.

MUHIMMANCIN BARCI

Samun wadataccen Barci a lokacin da ya dace, ya na da
matukar muhimmanci a jikin Mutum.
Alfanun Barci ga jikin mutum, ba shi da iyaka. Domin shi
ne akan gaba wajen taimakawa da kyakkyawan tunani da
nazari, kasancewa cikin koshin lafiya da daidaiton jiki, bugu da kari ya kan karawa mutum sa mun sararin kariya
daga afkuwar wasu ababe marasa dadi.
Yanayin da kake tsintar kan ka idan ka farka, shi yake
fassara halin da ka kasance a lokacin da ka ke Barci.
A sa'ilin da ake shakar barci, jikin mutum a cikin aiki yake
na gyara daidaiton al'amuran jiki da sinadaran cikin sa. Hakanan ya kan kare mutum daga kamuwa da cututtuka.
Kananan Yara da kuma ma su shekarun da ba su wuce
ashirin ba, barci ya kan taimaka musu wajen samun
girman jiki da kuzari.
Matsalar karancin barci ana cin karo da ita anan take.
Misali, Hatsarin Mota. Hakanan rashin barci na janyowa mutum rauni wajen
gane abubuwa a rayuwa, tangarda a gurin aiki, rashin
sakewa da jama'a, da kuma cudanya da abokan sana'a.
Wani binciken masana kiwon lafiya, ya nu na cewar idan
har Mutum ya na samun wadataccen barcin dare, ya kan
karawa mutum kaifin basira da koshin lafiya. Daga cikin illolin da rashin barci ke haifarwa akwai irin su
yawan son hayaniya da Jama'a, kokarin aikata miyagun
laifuka, rashin mayar da hankali akan muhimman
al'amura, raunin samar da shawara ko mafuta a
zamantakewa, da kuma rashin kambama matsayin da
mutum yake kai a rayuwa. A kiwon lafiya ma, rashin barci ba baya ba ne. Don ya na
taimakawa wajen saurin kamuwa da ciwon zuciya (don a
lokacin Barci, jijiyoyin da suke daukar jini zuwa zuciya da
sauran sassan jiki, sukan samu kwari sosai).
Hakanan Mutum ya kan iya kamuwa da ciwon Sukari. (A
sa'ilin da ake barci, sinadarin Insulin da yake da amfani a cikin sukarin da ke jini, ya kan samu matsala).
Bugu da kari, Mutum ya kan ji bala'in yunwa. Domin
sinadarin da yake sa yunwa (ghrelin) ya kan hauhawa ne,
idan ba'a barci, wanda kuma yake sa koshi (leptin) ya kan
yi kasa sosai.
Barci ya na da matukar amfani wajen kyautata balagar mutum, da kuma samun damar haihuwa.
A lokuta da yawa Mutane ba sa gane muhimmancin barci,
kuma a zahiri har hatsarurruka ya ke haddasawa, da suka
hada da na Jiragen Sama, Kasa, Ruwa, Motoci, da sauran
su.
Wani bincike ya nu na cewar duk shekara ana samun hatsari kimanin dubu dari, kuma akan yi asarar rayukan
mutane kusan dubu daya da dari biyar.
A takaice ana bukatar a duk kwana guda (awanni ashirin
da hudu), mutum ya samu wadataccen barci na awanni
bakwai ko takwas...
Nidai lokacin barcina yayi kai/ke fa??? Yi comment da halin da kake ciki kana kwance ne kana
niyar barci ko kaima sai gari yawaye

KIWON LAFIYA TA FUSKAR SANA'O'INMU

A haqiqanin gaskiya ba sana’ar da ba ta qunshe da gajiya da haxurra ga lafiyarmu sai dai wata ta fi
wata. A aikin walda ba idanu ne kaxai suke shan wahala
ba ga mai walda, duk inda tartsatsin narkakken qarfe ko
dalma ta tava a jikinka akwai illa ko dai ta quna ko wani
abu daban. Dole ke nan mai walda ya tanadi kayan da
za su rufe jiki gaba-xaya, domin kiyaye waxannan, muhimmi daga ciki shi ne gilashin rufe fuska gaba xaya
ba tabarau na ido kaxai ba. Kuma ba qanshin gaskiya a
ce wai ba zai tsufa da idonsa qalau ba, ko gajiyar sana’a
na tashi.
Sauran misalan da zan ba ku a xaya vangaren
tambayar, na irin wahalhalun da ke tattare da sana’o’inmu sun haxa da:
Noma: Wanda ake ce wa naduqe tsohon ciniki. Wataqila
saboda wahalarsa ce a yanzu yake nema ya zama tarihi.
Matsalolinsa sun haxa da yawan ciwon baya, kantar
hannu, shiga haxarin cizon qwari da dabbobi irinsu
kunama da maciji da sauransu. Sauran su ne saurin samun ciwon qaba, ko kwasar qwayoyin cuta a
kududdufai idan an je wanke jiki, qwayoyi irin masu
kawo tsargiya, kurkunu, dundumi da sauransu. Noman
zamani da ake yi ta hanyar na’urori kamar motar huxa
da ta shuka da ta girbi duk ba su tattare da irin wannan
haxari. Kiwo: Shi ma xan uwan noma ne kuma duk haxarin
noma zai iya shiga haxarin kiwo. Bugu da qari kuma ga
haxarin kamuwa da cututtukan dabbobi irinsu ciwon
barci ko sammore, wanda qudan tsando ke kawowa, ko
tarin TB na dabbobi da sauransu.
Su: Masunta suna cikin haxarin lumewa cikin ruwa ko shan gurvataccen ruwa mai qwayoyin cuta da kamuwa
da qwayoyin cuta irinsu tsargiya.
Jima: A yanzu da yake kamfanonin jima sun yi qaranci,
an xan rage samun cututtukan da ke faruwa sanadin
wannan matsala. Yawanci qwayoyin cuta ne ke taruwa
a kan fata idan an zo wanke su a kwashe su. A inda kamfanunnukan fata suka rage a kodayaushe
magudanan wurin ba sa rabo da ruwa mai wari wanda
ke xauke da nau’ukan qwayoyin cuta iri-iri, waxanda
kan iya shiga ruwan gari ta fasassun bututu, a samu
cututtukan ruwa irinsu amai da gudawa.
Rini: Marina suna xaya daga cikin mutanen da suka fi samun ciwon daji na mafitsara da dangoginsu,
sakamakon sinadaran haxi na yin rini. Wato shi tirin da
ake jiqawa wasu masana sun tabbatar yana iya kawo
ciwon daji.
Qira: Maqera kuma sun fi shiga haxarin raunuka da
qarafuna da quna daga garwashin wuta. Tuqi: A yanzu wannan sana’a ita ce za a ce ta fi kowace
sana’a haxarin cutarwa da ma rasa rayuka, domin nasu
kullum ne. Direbobi ko da ba ma na sana’a ba,
musamman masu tuqin nesa sun fi kowa samun karaya
da buguwa da sauran matsaloli na haxarurrukan qarfe
irinsu mutuwar wani vari na jiki da sauransu. Sana’ar wasanni: Duk da cewa wasanni na motsa jiki
suna xaya daga cikin sana’o’i masu gyara jiki da qara
lafiya, da wuya a samu cikakken xan wasan da bai tava
samun karaya ko targaxe ba.
Gini Da Injiniyanci: Magina da injiniyoyi suna xaya daga
cikin mutane masu samun haxurra su ma na buguwa da cutuwa daga injina ko matsalar kunne idan inji yana da
qara. Shanyewar sashen jiki sakamakon faxowa daga
sama ko kuma wani abu ya faxo wa mutum daga sama
kan faru. Ruwan fenti, wannan yana da sindarin dalma
da zai iya kawo illa ga lafiya.
Sayar da Abinci: Masu sayar da abubuwan ci da na sha kamar masu masu qosai da ma masu dafa abincin
sayarwa a gida waxanda suke amfani da murhu, suna
xaya daga cikin waxanda hayaqin itace ke wa illa a
huhu. An qiyasta cewa bayan taba sigari, masu girki a
gaban murhu su ne kan gaba wajen matsalolin huhu. Ba
nan hayaqin ya tsaya ba, yakan yi illa a ido ma. Kanikanci: Yawanci bakanikai ba wai datti ba ne yake sa
jikinsu da kayansu baqi, baqin mai ne kawai. Suna cikin
haxarin samun dusashewar fata dalilin wannan mai,
saboda ba kowane sabulu ba ne ke iya wanke shi amma
ban da duhun, ba wata illa yake ga ita fatar ba. Sai dai
duk da haka yana da kyau su ma su riqa rufe duka fatar tasu da dogayen kaya da sanya safar roba a
hannayensu, domin da dama haka suke cin abinci da
hannun ba tare da sun wanke su sosai ba, tunda duk
inda aka samu maiqo za a samu qwayoyin cuta.
Wanki da guga: Masu sana’ar wankau su kuma sun fi
kowa samun matsalar cin ruwa a fata saboda yawan hulxa da ruwa, sai kuma cin fata da sabulai ko omo kan
yi.
Ma’aikatan Ofis da ’Yan kasuwa: Masu iya magana suka
ce wai ‘zama wuri xaya tsautsayi inji kifi.’ Wannan
tsautsayi ba kan kifi kawai ya tsaya ba, waxanda suke
da sana’ar zama wuri guda na tsawon lokaci kamar masu aikin ofis da yawa-yawan ’yan kasuwa su kuma
sun fi kowa shiga haxarin kamuwa da cututtukan qiba
da na hawan jini da cututtukan zuciya saboda rashin
kazar-kazar, saboda ban da yawan zaman kuma kusan
sun fi kowa son cin ‘daxi.’
Aikin lafiya: A qarshe mu ma ba a bar mu a baya ba wajen samun matsalolin lafiya a wuraren aiki. Mu ma
namu haxurran ba qanana ba ne. Duk wanda ya zo da
qwayoyin cuta, yawanci a kanmu yake baje su, kamar
na tarin fuka da mura, ban da haxarin kamuwa da
cututtukan cikin jini irinsu qanjamau da ciwon hanta da
yawanci masu fixa ko xibar jini kan samu. Masu gajen haquri a dangin marasa lafiya a kanmu suke huce
haushinsu wajen faxa da masu jiyya har ma da bugun
kawo wuqa, duk da cewa wasunmu mu ma muna da
hannu wajen jawo faxa.
Waxannan misalai ne kawai, domin ba a tavo wasu da
dama ba irin masu sana’ar aikin ba-haya ba da masu sayar da fetur. Kowa idan ya tuna sana’a zai iya fito da
haxarin da ke tattare da ita. A taqaice dai duk inda ka
duba za ka ga akwai haxari ga lafiya tattare da kowace
sana’a, sai dai kawai a riqa xaukar matakan kariya daga
duk abubuwan da aka zayyana ga kowace sana’a,
wanda mun san masu karatun wannan shafi yanzu qwararru ne a wannan vangare. Mai aikin qarfi zai iya
shan maganin ciwon jiki irinsu panadol amma ban da
masu sa nacin sha da maye irinsu tramol.
(by doctor auwal bala)

RAYUWAR ALJANNAH *********************

Duk wanda yayi dacen shiga ALJANNAH, to hakika yayi
Arzikin da babu talauci bayansa. Kuma zaiyi rayuwar da babu mutuwa bayanta.. Kuma ya samu lafiyar da babu jinya bayanta.. Zai dawwama cikin samartaka wacce babu tsufa
bayanta... Kuma zai wanzu cikin Farinciki da annashuwa wacce babu
bakin-ciki ko damuwa bayanta... Kuma ya samu gamsuwar da babu Qosawa acikinta... 'Yan aljannah bassa fitsari ko ba-haya... Bassu kaki ko tari
acikinta... Furucinsu shine tasbeehi da tahmeedi izuwa ga
Ubangijinsu mai girma da daukaka.... Ga koramai nan suna gudana ko ta ina akarkashin
gidajensu. * Akwai Kogin ruwa mai dadin sha. Wanda idan kasha shi
ba zaka sake jin kishirwa ba har abada. * Akwai Qorama ta ruwan MADARA wacce batta tsami.
Kuma zaQinta ba zai misaltu ba. * Akwai kogin tatacciyar Zuma ingantacciya.. Wacce batta
Qarewa. * Akwai kogi na RUWAN GIYA.... Mai tsananin dadi wacce
idan ka kur'ba sai kaji NUTSUWA tana Qara zuwa maka.
(Sa'banin giyar duniya). * Akwai kogin ruwan Kafoor mai Qamshi. Wanda ba zai
misaltu ba. * Akwai kogin ruwan citta wanda yake bubbuga daga
SALSABEEL.. Akwai kowanne nau'I na 'ya'yan itace wadanda bazasu
Qare ba. Kowanne Dan Aljannah namiji. Yana da khadimai masu yi
masa hidima har guda (80,000) za'a aura masa mataye
guda 72 daga cikin HURUL-EEN. Mataye ne wadanda ido bai ta'ba ganin irinsu ba.. Hasken
fuskarsu yafi na hasken rana. Qamshin jikinsu yafi na duniya da dukkan abin-cikinta....

Shin Matar da ta auri Maza fiye da 1 ko 2, kuma dukkaninsu tayi musu biyayya, Idan sun shiga Aljannah gaba-dayansu, DA WANNE ZATA ZAUNA?

AMSA
>>>>>
Sayyidah Ummu Salamah - Matar Manzon Allah (saww)
Allah shi kara mata yarda, tayi masa irin wannan
tambayar. Amma ga amsar da ya bata nan: "YA UMMA SALAMAH, ZA'A BATA ZA'BI NE. KUMA ZATA ZA'BI
WANDA YAFI SAURAN KYAWAWAN DABI'U NE." "SABODA HAKA ZATA CE: YA UBANGIJINA! KA AURA MIN
WANNAN DOMIN YAFI KYAUTATA MIN FIYE DA SAURAN, TUN
AGIDAN ADUNIYA" YA UMMA SALAMAH!! HAKIKA KYAWAWAN DABI'U SUN
TATTARO ALKHAIRIN DUNIYA DANA LAHIRA" (IMAMUT TABRANEE NE YA RUWAITO HADISIN, KUMA IBNU
KATHEER MA YA KAWOSHI ACIKIN AN-NIHAYA FIL FITANI
WAL MALAHIMI). Don haka wannan amsar ta gamsar damu baki daya. WALLAHU A'ALAM.

BIYAYYAN MAI BIYAYYA, KO SA'BON MAI SA'BO, BAYA RAGYE KOMAI A CIKIN MULKIN ALLAH

Daga Abi Zarrin Al-Gifariyyu (RA) Daga Manzon
Allah (SAW) cikin irin abin da ya ke ruwaitowa
daga Allah cewa: Allah Yaa ce, "Yaa ku bayina!
hakika na haramta wa kaina zalunci ku ma na
haramta shi gare ku, to kada ku yi zalunci. Yaa
ku bayina! dukkanku 'batattu ne, sai wanda na shiryar. To, ku nemi shiriyata in shiryar da ku.
Yaa ku bayina! dukkanku mayunwata ne, sai
wanda na ciyar, to ku nemi ciyarwata in ciyar da
ku. Yaa ku bayina! dukanku huntaye ne, sai
wanda na tufatar. To, ku nemi tufarwata in
tufatar da ku. Yaa ku bayina! hakika kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai
baki daya. To, ku nemi gafarata, in gafarta muku.
Yaa ku bayina! ba za ku iya cutar da ni ba, balle
ku cuce ni, kuma ba ku isa amfanata ba, balle ku
amfane ni. Yaa ku bayina! da dai tun daga na
farkonku har ya zuwa na karshenku, da mutanenku, da Aljannunku, za su yi dai-dai da
zuciyar mafi tsoron Allanku, wannan ba zai 'kara
kome a cikin mulkina ba. Yaa ku bayina! da dai
tun daga na farkonku har ya zuwa na karshenku,
da mutanenku, da Aljannunku, za su yi dai-dai
da zuciyar mafi ashararancinku, wannan ba zai rage kome daga mulkina ba. Yaa ku bayina! da
dai tun daga na farkonku har ya zuwa na
karshenku, da mutanenku da aljannunku, za ku
taru a wuri guda, sannan ko wane 'daya ya roke
ni, ni kuma inba wa ko wane daya bukatarsa,
wannan ba zai ragye kome daga abin da na mallaka ba, sai kamar yadda allura za ta ragye
in an tsoma ta cikin kogi. Yaa ku bayina!
ayyukanku ne kurum nake 'kidaya muku, sannan
inba ku ladansu. To! wanda duk ya sami alkhairi
sai ya gode wa Allah, wanda kuwa ya sami
wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa". [Musulim].

MENENE YA ZAMA WAJIBI A KAN MU DANGANE DA SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W)?

Abin da ya zama dole a kan mu ga sahabban manzo Allah
(s.a.w) shine son su da neman Allah ya yarda da su, da
kuma kubutar da zuciyarmu da bakunanmu daga cutar da
su, da kuma yada falalarsu, tare da kamewa daga
mummunan abin da ya faru a tsakaninsu; Domin su ba
ma'asumai (mara sa laifi) ba ne, sai dai su masu kokari ne (Mujtahidai masu binciken gaskiya da nemanta). Duk
wanda ya dace daga cikinsu yana da lada biyu, amma idan
ya yi kuskure ya na da lada daya a kan kokarinsa
(Ijtahadinsa). Kuskurensa kuma an gafarta masa. Kuma
suna da kyawawan ayyuka wandanda za su tafiyar musu
da munanan da suka auku daga gare su, in ya auku. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "kar ku zagi sahabbaina, na
rantse da wanda raina ke hannunsa, da a ce dayanku zai
ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinare, ba zai kai
ciyarwar dayansu na mudun ko rabinsa ba." (Bukhari da
Muslim)
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wadda ya zagi sahabbaina to la'anar Allah da Mala'iku da mutane gaba
daya sun tabbata akansa" (twabarani)

Wednesday, 20 November 2013

WALIYYIN ALLAH

Waliyyi shi ne wanda ya yi imani da Allah, yake
kuma jin tsoronsa, kamar yadda Allah
Madaukakin Sarki ya fada a cikin littafinsa mai
girma, Suratu Yunus aya ta 62 - 63.
Dukkan musulmi mai tsoron Allah waliyyin Allah ne, gwargwadon imaninsa gwargwadon
walittakarsa, mafiya darajar waliyyai Annabawa
da Manzannin Allah, sai Sahabban Annabi
(S.A.W), Siddikai, shahidai sai Salihan bayi.
Babu wani zamani ko lokaci tun farkon zuwan
musulunci har zuwa daf da tashin Alkiyama da babu waliyyan Allah a cikinsa. Akwai waliyyan
Allah Mata kamar yadda ake samunsu a maza,
akwai waliyyan Allah a cikin malamai da masu
Mulki, da yan kasuwa, da talakawa da masu
kudi.
Ahlussunnati Wal Jama'a sun yi imani da samuwar waliyyan Allah, har ma karamominsu,
kamar yadda Alkur'ani da Hadisai ingantattau
suka tabbatar da hakan.
Walittaka bata haduwa da yin shirka da bokanci
ko da'awar komai Allah ne, duk wanda dayan
wadannan abubuwa na shirka ko bokanci ko da'awar komai Allah ne ya tabbata a kansa to
wannan ba waliyyin Allah ba ne, sai dai waliyyin
Shaidan.
Kuskure ne babba takaita waliyyan Allah akan
wasu mutane ko jama'a ko darika, a ce kadai a
cikinsu ake samun waliyyai. Haka nan kuskure ne ayyana wasu mutane ko mutum a ce duk
wanda baya sonsa ko baya son su, baya son
waliyyai, ko yana gaba da waliyyai, ko bai yarda
da waliyyai ba. Haka nan kuskure ne babba fitar
da sahaban Manzon Allah daga waliyyan Allah,
har a rika ganin mai kaunarsu baya son waliyyai, mai zaginsu da aibata su masoyin waliyyai ne,
tunda dai ya yarda da wasu mutane da ake
kirawa walittaka.
Kofar walittaka a bude take, babu wani mutum
da zai zama cikamakin waliyyan Allah, duk
wanda ya yi da'awar shi ne cikamakin waliyyai a yau ko a zamanin baya, hakika ya yi kuskure,
kuma ya fadi abin da ba haka yake ba,
cikamakin waliyyai shi ne karshen mumini da zai
bar wannan duniya. Allah ya sanya mu cikin
waliyyansa na gaskiya, masu kaunar waliyyan
gaskiya, Annabwa da Siddikai da Salihan bayi. Ameen.