Tuesday, 3 December 2013

SAYYIDUNA ABUBAKAR (RA).

SUNANSA: Abdullahi, Sunan mahaifinsa Uthman (Abu Quhaafa)
bn Amru, bn Ka'ab, bn Sa'ad, bn Taym, bn Murrah, bn Lu'ayy, bn
Ghalib, bn Fihr.. At-Taymiy Al-Qurashiy.

Nasabarsa ta hadu da ta Manzon Allah t(saww) daga kan
Kakansu mai suna Murratu bn Lu'ayyin.

MAHAIFIYARSA: Sunanta Ummul-Khayri (Salma) bnt Sakhr, bn
Ka'ab, Sa'ad, bn Taymin bn Murrah.

HAIHUWARSA: An haifeshi ne bayan shekaru 2 da 'yan watanni
da haifuwar SHUGABAN HALITTA (saww).

Ance ainahin sunansa ABDUL-KA'ABAH (wato bawan ka'abah).
Amma bayan zuwan Musulunci sai Manzon Allah (saww) ya
chanja masa sunan Zuwa ABDULLAHI..

ALKUNYARSA: Shine sunan da kowa yafi saninsa dashi. wato
ABUBAKRIN.

LAQABINSA: yana da lakabobi masu yawa. amma mafi shahara
daga ciki shine: ★ASSIDDEEQ. (mafi gaskatawa) Allah da kansa ya kirashi da wannan sunan acikin Suratuz
Zumar ayah ta 33. ★ SAHIBUN NABIYYI (SAWW): (abokin Annabi saww) Allah ne DA
KANSA ya sanya masa wannan sunan acikin ALQUR'ANI cikin
Suratut-Tauba ayah ta 40.

AL-ATQAA: (mafi tsoron Allah) Allah ne ya sanya masa wannan
sunan acikin Suratul Layli ayah ta 17 da 18.

AL'ATEEQ: ('yantacce) Manzon Allah ne (saww) ya sanya masa
wannan sunan alokacin da yace masa "KAI 'YANTACCE NE DAGA
WUTA". (ba zaka shigeta ba Ya Ababakr). YA ALLAH KA QARA MASA YARDA. Mu kuma ka bamu albarkarsu,
ka nufemu da koyi dasu acikin ayyukanmu da zantukanmu.

No comments:

Post a Comment