Tuesday, 10 December 2013

WANENE DUJAL? =============

Masih Ad-Dajjal wani mutum ne daga cikin halittun Allah. yana
da Siffar 'yan Adam amma sai dai yafi 'yan Adam girman jiki.

Ajikin Fuskarshi yana da ido Qwalli daya ne. ba guda biyu
kamar namu ba ..

Yanzu haka chan acikin wani kogo ko kuma Gida abakin Bshrul
Muheet.(ko kuma sham awata ruwayar).

An daureshi da Ankwa.. kamar yadda wani Sahabin Manzon
Allah (saww) mai suna Tameemud Dary ya ganshi harma sunyi
maganganu dashi.

Hadisai da dama sun tabbatar mana da cewar Dujal zai
bayyana ne achan Qarshen Zamani. gab da tashin Alkiyamah. Zai zo ya rayu aduniya gwargwadon kwana 40 ne Kwana daya
daga ciki yakai kamar tsawon shekara guda. wani kwana dayan
kuma kamar tsawon wata guda.sauran kwanakin kum kamar
irin ranaikun mutanen duniya ne .

Fitinar Dujal ita ce mafi girman fitinar Qarshe Zamani. YA ALLAH KA TSAREMU KA KIYAYEMU DON DARAJAR ALQUR'ANINKA
MAI GIRMA.

SAYYIDUNA ABUBAKRIN (3) ------------------------------------

KHALIFAN MANZON ALLAH (saww)
Azamanin Khalifancinsa, bayan wafatin Manzon Allah (saww)
Farkon annobar data fara kunnowa kai ita ce: RIDDA da
yawancin larabawan Qauyuka suka rika yi. Mafiya yawansu daga jin cewar Manzon Allah (saww) yayi
wafati shikenan sai sukayi ridda suka fice daga Musuluncin. Wasu kuma basu bayyana cewar sun fita daga Musuluncin ba,
sai dai sun Qi bayar da zakkah.
Wasu kuma bayan riddar ma, har sun fara da'awar Annabta.
Irinsu Musaylamah Alkazzab. Har sai da ya zama iya garuruwa 3 ne kadai ake yin Musulunci
aduniya. Wato Makkah, Madeenah, da Ta'if. Amma matakin farko da ya fara yi shine zartar da abubuwan
da Manzon Allah (saww) ya riga ya fara su. Misali kamar tashin
rundumar Usamah bn Zaid bn Harithah zuwa yakin Rum. Da yawa daga cikin Sahabbai sunyi niyyar hanashi tura wannan
rundunar. Saboda ganin halin da ake ciki. Yayin da Sayyiduna Umar (ra) ya tareshi ya gaya masa cewar
bai kamata atura wannan rundunar ba.
Sai ya bada amsa cewar: "Wallahi ni bazan kunce duk wani abinda Manzon Allah (saww)
ya Qulla ba. Koda tsuntsaye da Zakokin gefen Madina zasu rika
kawo mana hari suna cinyemu daya bayan daya" Ya Qara da cewar: "Wallahi koda zakoki zasu cinye Ummuhatul
Mu'umineena, wallahi sai na tashi rundunar Usamah" Da sauran Manyan Sahabbai suka ga babu makawa awajen
Sayyiduna Abubakrin, sai suka sake bashi wata shawarar. Suka
ce masa: "to me zai hana ka chanza Komandan rundunar? Ka
cire Usamah ka sanya wani wanda yafi shi yawan
shekaru?" (Saboda shi Usama yaro ne matashi asannan) Daga jin wannan shawarar tasu sai ransa ya baci. Yake ce musu:
"Ta yaya za'a chanza hukuncin da Manzon Allah (saww) ya riga
ya zartar?"
Saboda haka ya tura wannan rundunar Qarkashin jagorancin
Sayyiduna Usamatu bn Zaid. Suka fita suka tafi suka yaki
rundunar Rumawa. Suka samo gagarumar nasara. Suka zauna
Kwana 70 ko 40 awata ruwayar. Sannan suka dawo gida. Wannan fitar tasu da dawowarsu ya tsorata Larabawan
Qauyuka wadanda sukayi ridda. Don haka da dawowarsu sai Sayyiduna Abubakrin (Khalifan
Manzon Allah saww) ya tura su yaki da 'yan ridda da kuma
masu hana zakkah.

MARTABOBIN ABUBAKRIN (2) ••••••••••••••••••••••••••••••••••

12. Aranar Alkiyamah idan anzo shiga Aljannah, Sayyiduna
Abibakrin shine na farkon shiga acikin wannan Al'ummar.
bayan Manzon Allah (saww).

13. Idan yazo shiga Aljannah, Mala'iku zasu rika kiransa ta
kowacce Qofa daga cikin Qofofin gidan Aljannah. (kamar yadda
Annabi *saww* yayi masa albishir).

14. Shine mafi Soyuwar Mutane awajen Manzon Allah (saww).
kamar yadda yazo acikin hadisin Amru ibnul Aas (ra).

15. Tun azamanin Jahiliyya Sayyiduna Abubakrin bai ta'ba yin
sujjadah ga gunki ba.

16. Tun kafin zuwan Musulunci Sayyiduna Abubakrin ya
haramtawa kansa shan giya. bai ta'ba sha ba tunda yake. (rta).

17. Tun kafin zuwsn musulunci Buhaira yayi masa albishir
cewar shi zai zama aboki kuma Khalifan Annabin Qarshe
(saww).!!!Hakika duk wadanda suka yima Musulinci aiki basu kai
Abubakar ba... Hakika duk wanda ya hidimtawa MANZON ALLAH (saww), to bai
kai ABUBAKAR BA. Hakika duk wani masoyin Annabi (saww) bai kai ABUBAKAR BA. Shine ya gaskata Manzon Allah (saww) alokacin da yawancin
mutane suke Qaryatashi. Shine yaso Manzon Allah (saww) alokacin da yawancin mutane
suke Qinsa.. Saboda Zurfin soyayyarsa ga Manzon Allah (saww) shi yasa
IMANINSA MA YAFI NA KOWA ZURFI. Ya Allah ka Qara tsira da aminci abisa Annabin Rahama (saww)
da iyalan gidansa da DUKKAN Sahabbansa.

Tuesday, 3 December 2013

FA'IDAR YIN QAHO

Yin Qaho, abu ne mai kyau a addinin Musulunci. Kuma Sunnah
ne daga Sunnonin Manzon Allah (saww). Annabi (saww) yayi Qaho. Kuma ya umurci al'ummarsa su rika
yin Qaho. Kuma ya fadi fa'idodin yinsa. Kamar yadda zamu
gani acikin wadannan hadisan masu zuwa:

1. FA'IDAR YIN QAHO
-----------------------------
akwai hadisai da dama wadanda sukazo da maganar fa'idodin
yin Qaho. Ga wasu daga ciki.

Sayyiduna Ibnu Abbas (rta) ya ruwaito cewar: "Manzon Allah
(saww) yace: "Za'a samu warkaswa ne acikin abubuwa guda 3:
1. Shan Zuma, 2.Askar mai yin Qaho, 3.da kuma sakiya da wuta"
(Sahihul Bukhary 10/136)

2. Abu Huraira (rta) ya ruwaito cewar Manzon Allah (saww)
yace: "Duk wanda akayi masa Qaho aranar 17 ko 19 ko 19 ga wata,
Allah zai warkar dashi daga dukkan cututtuka" (Aduba sunanu Abi Dawood, hadisi na 3861. Da kuma Baihaqee,
juzu'I na 9 shafi na 340).

MUHIMMANCIN QAHO
**********************
Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) ya ruwaito cewar YA GA ANYI
MA MANZON ALLAH (SAWW) QAHO, KUMA HARMA BIYA KUDI YA
SALLAMI MAI YIN QAHON"
(Aduba Sahihu Muslim hadisi na 1202).

Hakanan Sayyiduna Anas bn Malik (ra) shima ya ruwaito cewar
yaga wani mutum mai suna ABU TAYYIBAH yayi wa MANZON
ALLAH (saww) Qaho. Har ma Manzon Allah (saww) yayi umurnin
cewa aba ma mutumin mudu biyu na abinci.
(Sahihu muslim hadisi na 1577).

Har ila yau akwai wani hadisin daga Anas bn Malik (ra) cewar
Manzon Allah (saww) yace: "Adaren da akayi Isra'I dani, babu wata Jama'ar (Mala'iku) dana
wuce, fache sai sunce min: "YA MUHAMMADU KA UMURCI
AL'UMMARKA SU RIKA YIN QAHO". (Ibnu Maajah ne ya ruwaito).

MARTABOBIN ABUBAKRIN ======================

Hakika acikin wannan al'ummar ta Annabin Qarshe, babu wani
mutum Guda 'daya wanda ya samu tarin Martabobi irin na
Sayyiduna Abubakrin Assiddeeq (rta).
Ga wasu daga cikin martabobin kamar haka:

1. Shine wanda Allah ya zabeshi ya fara yin Imani da Manzon
Allah (saww).

2. Shine wanda Allah ya zabeshi domin yin rakiyar Annabinsa
Fiyayyen Halittu (saww) alokacin hijira.

3. Shine wanda ya sadaukar da dukiyarsa baki daya domin
hidimar musulunci. fiye da kowa. kuma tun kafin kowa.

4. Shine yafi dukkan Sahabbai (rta) acikin TSANANIN SON ANNABI
(saww).

5. Shine wanda yafi kowa Zurfin Imani da gaskatawa. kamar
yadda Allah da Manzonsa (saww) yayi masa shaidar haka.

6. Shine kadai wanda ya bama Manzon Allah (saww) 'yarsa
BUDURWA ya aura.

7. Manzon Allah (saww) yace mai "KAI 'YANTACCE NA DAGA
WUTA" (ba zaka shigeta ba).

8. Manzon Allah (saww) yayi masa bushara da cewar SHI DAN
ALJANNAH NE.

9. Manzon Allah (saww) yakan yi fushi mai tsanani idan an ta'ba
Sayyiduna Abubakrin (rta).

10. Manzon Allah (saww) yayi musu bushara dashi da Sayyiduna
Umar (ra) cewar sune SHUGABANNIN DATTIJAI NA GIDAN
ALJANNAH.

11. Shine Farkon Khaleefan Manzon Allah (saww).

IYALAN SAYYIDUNA ABUBAKAR ------------------------------------------

Sayyiduna Abubakrin ya auri Mataye guda hudu ne arayuwarsa
gaba daya. Guda biyu ya auresu ne tun zamanin Jahiliyya.
Sune:

1. QUTAILAH bnt ABDIL-UZZA : ta haifa masa 'ya'ya biyu.
Abdullahi da Asma'u (ra).

2. UMMU RUMAN bnt AAMIR ALKINAANIYYAH : ta haifa masa
Abdurrahman da A'ishah (ra).

*Sai kuma azamanin Musulunci ya auri wasu matayen guda 2.
Sune:
3. HABIBAH bntul KHAARIJAH AL-ANSARIYYAH : ya rasu ya barta da
ciki, ta haifa masa Ummu Kulsum bayan rasuwarsa.
4. ASMA'U bintu UMAYSIN : ta haifa masa mai sunan Ma'aiki
(saww) wato MUHAMMAD bn ABIBAKRIN (ra). Wanda ya zamto
daya daga cikin jagororin Musulunci.

Gaba daya dai matan da ya aura guda 4 ne. Kuma 'ya'yansa
aduniya guda 6 ne.

Ya aurar da 'yarsa ASMA'U izuwa ga babban Sahabin Manzon
Allah (saww) kuma 'Dan uwan Manzon Allah (saww) wato
Sayyduna AZZUBAIRU ibnul AWWAAM (ra). Harma ta haifa masa
yaro namiji bayan hijira zuwa madinah. Wato Abdullahi bn
Zubair (ra).
Wanda ya zamto Babban kogin ilimi kuma gwarzon mayaki.
Kuma ya samu addu'a daga Manzon Allah (saww).
SAYYIDAH A'ISHA (rta) ya aurar da ita izuwa ga Babban
Masoyinsa, kuma Shugabansa, wato Manzon Rahama (saww). Ta zauna tare da Manzon Allah (saww) har zuwa wafatinsa.
Kuma ita ce mafi soyuwa agareshi aduk cikin matayensa. Kuma ta kwaso ilimai masu tarin yawa daga wajensa. Harma
acikin dukkan mataye babu kamarta wajen yawan hadisai, da
kuma sanin tarihi da nasaba, da kuma fasahar harshen larabci. Ya Allah ka Qara yarda agaresu baki daya.

SAYYIDUNA ABUBAKAR (RA).

SUNANSA: Abdullahi, Sunan mahaifinsa Uthman (Abu Quhaafa)
bn Amru, bn Ka'ab, bn Sa'ad, bn Taym, bn Murrah, bn Lu'ayy, bn
Ghalib, bn Fihr.. At-Taymiy Al-Qurashiy.

Nasabarsa ta hadu da ta Manzon Allah t(saww) daga kan
Kakansu mai suna Murratu bn Lu'ayyin.

MAHAIFIYARSA: Sunanta Ummul-Khayri (Salma) bnt Sakhr, bn
Ka'ab, Sa'ad, bn Taymin bn Murrah.

HAIHUWARSA: An haifeshi ne bayan shekaru 2 da 'yan watanni
da haifuwar SHUGABAN HALITTA (saww).

Ance ainahin sunansa ABDUL-KA'ABAH (wato bawan ka'abah).
Amma bayan zuwan Musulunci sai Manzon Allah (saww) ya
chanja masa sunan Zuwa ABDULLAHI..

ALKUNYARSA: Shine sunan da kowa yafi saninsa dashi. wato
ABUBAKRIN.

LAQABINSA: yana da lakabobi masu yawa. amma mafi shahara
daga ciki shine: ★ASSIDDEEQ. (mafi gaskatawa) Allah da kansa ya kirashi da wannan sunan acikin Suratuz
Zumar ayah ta 33. ★ SAHIBUN NABIYYI (SAWW): (abokin Annabi saww) Allah ne DA
KANSA ya sanya masa wannan sunan acikin ALQUR'ANI cikin
Suratut-Tauba ayah ta 40.

AL-ATQAA: (mafi tsoron Allah) Allah ne ya sanya masa wannan
sunan acikin Suratul Layli ayah ta 17 da 18.

AL'ATEEQ: ('yantacce) Manzon Allah ne (saww) ya sanya masa
wannan sunan alokacin da yace masa "KAI 'YANTACCE NE DAGA
WUTA". (ba zaka shigeta ba Ya Ababakr). YA ALLAH KA QARA MASA YARDA. Mu kuma ka bamu albarkarsu,
ka nufemu da koyi dasu acikin ayyukanmu da zantukanmu.